Friday, November 6, 2026
HomeSiyasaAPC ta kalubalanci Kwankwaso ya babatar da hujjoji kan zargin tsoma bakin...

APC ta kalubalanci Kwankwaso ya babatar da hujjoji kan zargin tsoma bakin Abba a harkokin INEC

Ofishin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC na jihar Kano ya buƙaci Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da ya gabatar da hujjoji kan zargin da yake yi wa Gwamna Abba Kabir Yusuf na tsoma baki a harkokin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), domin hana amincewa da ɗan takarar gwamnan jam’iyyar NDC a zaɓen 2027.

Sanarwar da kakakin ofishin yaƙin neman zaɓen, Hon. Sanusi Majidadi Ƙiru, ya fitar a ranar 2 ga Nuwamba, 2026, ta mayar da martani kan kalaman Kwankwaso, ciki har da zargin cewa Gwamna Abba yana nadamar ficewa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.

A cewar sanarwar, APC ta tunatar da Kwankwaso cewa a zaɓen gwamnan Kano na 2019, lokacin da shi da Abba suke jam’iyyar PDP, takarar Abba ta fuskanci ƙalubalen shari’a.

Ta ce Babbar Kotun Tarayya ta yanke hukunci a ranar 4 ga Maris, 2019, kafin Kotun Ɗaukaka Ƙara ta bayar da umarnin dakatar da aiwatar da hukuncin a ranar 8 ga Maris, kwana guda kafin zaɓen gwamnan.

Haka kuma, APC ta ce matsalolin tantance ’yan takara da ƙalubalen shari’a ba su tsaya ga jam’iyyar NDC a Kano kaɗai ba.

Ta yi nuni da bayanan INEC da suka nuna cewa hukumar ta samu ƙorafe-ƙorafen takarar gwamna guda 69 daga jam’iyyun siyasa 12 a jihohi 26, inda aka amince da guda 41, aka kuma ƙi amincewa da guda 28.

Dangane da zargin cewa Gwamna Abba yana nadamar komawa APC, ofishin yaƙin neman zaɓen ya ce gwamnan ya bayyana dalilan sauya sheƙarsa a fili, waɗanda suka haɗa da haɗin gwiwar siyasa, zaman lafiya da muradun ci gaban Kano.

APC ta ƙalubalanci Kwankwaso da ya gabatar da hujjojin da ke danganta Gwamna Abba da takunkumin shari’ar da ya shafi tikitin NDC a Kano, maimakon yin zarge-zarge marasa hujja.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments