Shugaban rukunin kamfanonin BUA, Abdulsamad BUA, ya bayyana cewa ya samu ziyarar bazata daga tsohuwar matarsa, Ministar Al’adu da Tattalin Arzikin Ƙirƙire-ƙirƙire ta Najeriya, Hannatu Musawa, a ofishinsa da ke Abuja.
A wani saƙo da ya wallafa, BUA ya ce duk da sauye-sauyen da lokaci ke kawowa, abota da mutunta juna suna nan daram a tsakaninsu.
Ya bayyana farin cikinsa kan ganawa da Musawa, yana mai yabawa da himma da sadaukarwar da take nunawa wajen bunƙasa al’adu da tattalin arzikin masana’antun ƙirƙire-ƙirƙire na Najeriya.
Ya kuma yi mata fatan ci gaba da samun nasara a ayyukanta na hidimtawa ƙasa.