Masu zuba jari daga ƙasashe 120 sun sayi hannayen jarin matatar man Dangote da ke Legas, kamar yadda katafaren kamfanin ya bayyana, bayan sayar da hannayen jarin ya samu kuɗaɗen da suka ninka adadin da aka yi hasashe sau uku.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa kamfanin Dangote ya sanar da nasarar sayar da hannayen jarin, bayan tsawaita lokacin cinikin da ƙarin makonni biyu, wanda aka kammala a ranar Talata.
Rahotanni sun bayyana cewa kamfanin ya shirya sayar da kashi 30 cikin 100 na hannayen jarin matatar a kan dala biliyan 1.6, amma kuɗaɗen da aka nema sun haura wannan adadi har sau uku.
Kamfanin Dangote ya bayyana nasarar a matsayin babbar nasara ga nahiyar Afirka, yana mai cewa haɗin kai tsakanin ’yan Afirka na iya buɗe ƙofofin manyan nasarori a fannin kasuwanci da zuba jari.
Dangote ya ce masu zuba jari daga dukkan ƙasashen Afirka 54 sun shiga cinikin, yayin da wasu masu zuba jarin suka fito daga sauran nahiyoyin duniya.
Matatar ta Dangote, wadda aka gina a Legas kan kuɗin da ya kai dala biliyan 20, tana da ƙarfin tace ganga 700,000 na mai a kowace rana. Kamfanin na shirin faɗaɗa ta domin ƙara ƙarfin tace man zuwa ganga miliyan 1.4 a kowace rana, wanda zai iya mayar da ita cikin manyan matatun mai a duniya.
Kamfanin ya kuma sanar da cewa za a fara bai wa masu zuba jari hannayen jarin da suka saya daga makon gobe, kafin a sanya su cikin kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya.