Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga Majalisar Dokokin Jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa.
Sauran wanda aka miƙa sunansa shi ne Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance su ranar Talata, 3 ga Nuwamba, 2026, da ƙarfe 10:00 na safe.
Kakakin Majalisar, Kamaluddeen Sani Shawai, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, inda ya ce Gwamna Abba ne ya aika da wasiƙar neman a tantance mutanen biyu.
Sanarwar ta ce za a gudanar da tantancewar ƙarƙashin jagorancin Shugaban Majalisar, Rt. Hon. Jibril Isma’il Falgore, bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Najeriya.