Wasu rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojoji sun yi nasarar fatattakar wasu ’yan ta’adda a yankin Kwanan Barau, da ke tsakanin Tegina da Zungeru, a kan hanyar Kontagora zuwa Minna, da safiyar yau.
Rahotanni sun ce an hallaka wasu daga cikin ’yan ta’addan bayan sun yi ƙoƙarin tsallakawa ta kan hanyar. Sai dai, sakamakon tsananin ruwan wutar da suka fuskanta daga dakarun sojin, lamarin ya tilasta musu komawa ta hanyar da suka fito.
Wasu daga cikin ’yan ta’addan sun mutu yayin arangamar, yayin da wasu kuma suka tsere dauke da munanan raunuka kamar yadda Gaskiya News Hausa ta ruwaito.
Mazauna yankin sun yaba wa jami’an tsaron bisa yadda suka tunkari ’yan ta’addan, inda aka shafe sama da sa’o’i biyu ana musayar wuta tsakanin ɓangarorin.
A halin yanzu, rahotanni sun ce an samu nasarar buɗe hanyar, bayan da jami’an tsaron suka fatattaki ’yan ta’addan daga yankin.