Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaKu yafe wa Tinubu da Abba Kabir Yusuf idan sun bata muku...

Ku yafe wa Tinubu da Abba Kabir Yusuf idan sun bata muku – Alhassan Ado Doguwa

Alhassan Ado Doguwa na wannan batu ne yayin da babban zaben 2027 ke kara karatowa a Najeriya

Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Tudun Wada/Doguwa, Alhassan Ado Doguwa, ya ƙara kaimi wajen yaƙin neman zaɓe domin jam’iyyarsa ta APC ta yi nasara a 2027.

A wani bidiyo da aka wallafa a shafin Siyasarmu na Facebook, Doguwa ya kuma yi magana kan sulhun da aka yi tsakaninsa da Air Commodore Salisu Yusha’u Soja mai ritaya da matarsa, Hon. Sa’adatu Salisu Soja.

Doguwa ya ce ba ya shakkar cewa Salisu Soja da matarsa za su cika alkawarin da suka ɗauka bayan sulhun da aka yi tsakaninsu.

Da yake kira ga al’ummar Yar Mariya da sauran sassan mazabarsa, Doguwa ya buƙace su da su bai wa APC cikakken goyon baya a zaɓen 2027 ba tare da wani sharadi ba.

“Ina roƙonku da alfarmar arziki, kamar yadda kuka yarda da ni, ina roƙonku ku je ku riƙe amanar APC daga sama har ƙasa.

Doguwa ya kuma roƙi magoya bayansa da su yafe wa Shugaba Bola Tinubu da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, idan har sun taɓa yin abin da ya ɓata musu rai.

Ya ce yana neman afuwar ne a madadin shugabannin, yana mai cewa akwai yiwuwar ba za su samu damar haɗuwa da dukkan talakawansu domin neman gafara da kansu ba.

Ya kuma yi kira ga ’ya’yan APC da su riƙa yi wa ƙasa da Shugaba Tinubu addu’ar samun nasara wajen sauke nauyin da ke kansa. Haka kuma, ya ce ya kamata a yi wa Gwamna Abba Kabir Yusuf addu’a domin ya samu damar gudanar da ayyukan da za su amfani al’ummar Kano.

Da yake bayyana dalilin da ya sa yake goyon bayan sake zaɓen Tinubu, Doguwa ya ce Najeriya ba ta ƙunshi Arewa kaɗai ba, don haka ya kamata a bai wa yankin Kudu damar jagorantar ƙasar.

Ya ce Tinubu bai yi watsi da wasu manyan ayyukan da gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ta fara a Arewa ba. A matsayin misali, ya ambaci aikin hanyar Abuja zuwa Kano, yana mai cewa saura kaɗan a kammala aikin.

A cewarsa, gwamnatin Tinubu ta karɓi kwangilar aikin daga kamfanin da aka bai wa aikin tun farko ne domin tabbatar da kammala babbar hanyar.

Doguwa ya kuma ce saboda muhimmancin hanyar da ta haɗa sassa daban-daban na ƙasar, gwamnatin tarayya ta fara aikin titin Badagry zuwa Sokoto.

Ya ce ya ziyarci wurin da ake gudanar da aikin, inda ya ga yadda aikin ke gudana, yana mai cewa ana sa ran hanyar za ta kai har zuwa Sokoto daga Legas.

Har ila yau, Doguwa ya ce gwamnati ta ware kuɗaɗe domin haɗa Najeriya da Jamhuriyar Nijar ta hanyar layin dogo, inda ya bayyana cewa aikin ya riga ya samu ci gaba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments