Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiLabaraiLauyoyi sun fafata kan hurumin kotu a shari’ar Sheikh Lawan Triumph

Lauyoyi sun fafata kan hurumin kotu a shari’ar Sheikh Lawan Triumph

Babbar Kotun Shari’a da ke Kofar Kudu a Kano ta yi fatali da ƙalubalen huruminta na sauraron ƙarar da wasu ƙungiyoyin Musulunci suka shigar kan Malam Lawan Abubakar Triumph.

Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ne ya jagoranci zaman kotun, inda ya yi watsi da hujjojin lauyan wanda ake ƙara, Barista Abdurrazak Ahmad, na neman kotun ta yi watsi da shari’ar saboda rashin hurumi.

Tun da farko, lauyan Sheikh Lawan ya yi zargin cewa ƙungiyoyin da suka shigar da ƙarar sun taɓa gabatar da makamanciyar ƙara a Babbar Kotun Jihar Kano.

Ya kuma ƙalubalanci sahihancin ikon ƙungiyoyin na shigar da ƙarar, yana mai cewa ba su gabatar da shaidar rajistarsu ba.

Lauyan ya kuma yi iƙirarin cewa batun ya shafi hurumin Babbar Kotun Tarayya ne, ba Kotun Shari’a ba.

Sai dai lauyan masu ƙara, Barista Aliyu Usman Haji, ya musanta waɗannan hujjoji, yana mai cewa Kotun Shari’a tana da hurumin sauraron ƙarar.

Ya kuma buƙaci kotun ta umarci ’yan sanda su gudanar da bincike kan zargin ɓatanci ga addinin da ake yi wa malamin.

Barista Haji ya gabatar wa kotun da takardun rajistar ƙungiyoyin, yana mai cewa ba a gabatar da su a baya ba ne saboda ba a buƙace su a wancan lokacin.

Bayan sauraron hujjojin ɓangarorin, Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ya yi fatali da ƙalubalen hurumin kotun, tare da amincewa a ci gaba da sauraron shari’ar.

Kotun ta kuma umarci masu ƙarar su gabatar da kwafin takardun rajistar ƙungiyoyin domin a duba su, kafin a sanar da ranar ci gaba da sauraron ƙarar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments