Ministan Aikin Gona da Samar da Abinci, Abubakar Kyari, ya ce farashin wasu muhimman kayan abinci ya ragu da kusan kashi 50 cikin 100 idan aka kwatanta da farashinsu kafin shekarar 2023.
Kyari ya bayyana hakan ne ranar Litinin a Maiduguri, yayin bude taron Community of Practice Meeting da ya haɗa kwamishinonin da ke kula da harkokin noma, lafiya, muhalli da raya karkara daga sassan Najeriya.
Ma’aikatar Aikin Gona da Samar da Abinci ta Tarayya ce ta shirya taron tare da Gwamnatin Jihar Borno, da tallafin gwamnatin Jamus.
Taken taron shi ne “Ƙarfafa haɗin gwiwa domin samar da isasshen abinci a Najeriya”, inda aka mayar da hankali kan ƙarfafa samar da abinci da tabbatar da wadatar abinci a Najeriya.
Kyari ya ce manufar gwamnatin tarayya ita ce ƙara yawan abincin da ake samarwa, rage farashin abinci, ƙarfafa tattalin arzikin karkara da kuma samar da tsarin abinci mai jure matsaloli.
Ya ce, “Mun ga raguwar farashin wasu muhimman kayan abinci da ya kai kashi 50 cikin 100, tare da ƙara samar da kayan noma, zuba jari a ababen more rayuwa na karkara da kuma tallafa wa ƙananan manoma.”
Ministan ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta mayar da batun samar da isasshen abinci cikin manyan abubuwan da take bai wa muhimmanci.
Ya kuma bukaci ’yan Najeriya su yi amfani da bayanan da ake da su wajen tantance ayyukan gwamnati, maimakon mayar da hauhawar farashin rayuwa batun siyasa.
Kyari ya ce, “Mu kasance masu gaskiya, nawa ne buhun shinkafa da masara a shekarar 2023, kuma nawa ne yanzu? Kashi nawa ne bambancin? Kada mu mayar da waɗannan abubuwa batun siyasa.”