Gwamnan Jihar Oyo kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APM, Seyi Makinde, ya ce zaɓen shugaban ƙasa na 2027 zai kasance fafatawa tsakanin jam’iyyar APC mai mulki da ’yan Najeriya, ba wai tsakanin jam’iyyun siyasa kawai ba.
Makinde ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Katsina, yayin wani taron tattaunawa da jama’a na yankin Arewa maso Yamma, wanda ƙungiyar yaƙin neman zaɓensa ta shirya domin gabatar da shirin jam’iyyar mai taken “Reset Nigeria”.
A cewar rahoton Daily Trust, Makinde ya yi kira ga ’yan Najeriya da su tabbatar sun mallaki katin zaɓensu na dindindin (PVC), tare da amfani da shi wajen kaɗa ƙuri’a a zaɓen da ke tafe.
Ya ce amfani da ƙuri’a yadda ya kamata na daga cikin hanyoyin da ’yan ƙasa za su iya bayyana ra’ayinsu kan shugabanci da kuma makomar ƙasar.