Matatar man Dangote da wasu dillalan man fetur sun rage farashin man fetur a wuraren ajiyar mai da ke Legas, Fatakwal, Calabar da Warri, biyo bayan sauyin farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya.
Rahoton da shafin Petroleumprice.ng ya wallafa ya nuna cewa an fi samun sauyin farashin a Legas, inda wasu masu rumbunan ajiyar mai suka rage farashin fetur da tsakanin N20 zuwa N24 kan kowace lita.
Rahoton ya ce wannan sauyi na farashin na zuwa ne yayin da farashin gangar ɗanyen mai na Brent ke kusan dala 100 a kasuwar duniya, yayin da farashin ɗanyen mai na West Texas Intermediate (WTI) ya koma dala 91.17 kan kowace ganga.
A Legas, Matatar Dangote ta rage farashin litar fetur daga N1,350 zuwa N1,325, wanda ke nufin an samu ragi na N25 a kan kowace lita.
Haka kuma, kamfanonin dillancin mai na Ascon Integrated da Pinnacle sun rage farashin fetur ɗinsu da N24, inda suka koma sayar da litar kan N1,326 da N1,327 bi da bi.