Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce jam’iyyarsu za ta sake duba batun tallafin man fetur tare da samar da tsarin da ya ce zai fi dacewa, idan suka samu nasara a zaɓen 2027.
Maganar ta zo ne bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Peter Obi, ya bayyana cewa ba shi da ra’ayin dawo da tallafin man fetur.
Batun tallafin man fetur na daga cikin muhimman batutuwan da ke cikin muhawarar siyasar Najeriya yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.