Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) ta tura Abdullahi Salisu Kabara a matsayin sabon kwamandan hukumar a Jihar Neja.
Kabara ya maye gurbin Commandant Suberu Siyaka Aniviye, wanda aka dakatar kan mutuwar masu haƙar ma’adinai 37 da suka mutu a hannun hukumar yayin da ake tsare da su.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar a jihar, DSC Abubakar Rabiu Muti, ya ce Kabara ya karɓi ragamar aiki a wani lokaci mai matuƙar muhimmanci ga hukumar sakamakon lamarin.
Sabon kwamandan ya bayyana alhininsa kan mutuwar mutanen, tare da mika ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasu da sauran waɗanda lamarin ya shafa.
Ya ce yayin da hukumar ke ci gaba da ayyukanta na yaƙi da haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, kare rayuka da mutunta mutanen da ke tsare a hannun hukuma ya kasance muhimmin nauyi.