Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Tarayya ta dakatar da jami’an NSCDC 20 kan mutuwar masu haƙar...

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da jami’an NSCDC 20 kan mutuwar masu haƙar ma’adinai

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da jami’an Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) 20, tare da kwamandan hukumar na Jihar Neja, Suberu Aniviye, kan mutuwar mutane 37 da ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a hannun hukumar.

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da jami’an Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) 20, tare da kwamandan hukumar na Jihar Neja, Suberu Aniviye, kan mutuwar mutane 37 da ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a hannun hukumar.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce matakin ya biyo bayan umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa da gaskiya kan lamarin.

Ya ce an kafa kwamitin bincike domin gano musabbabin mutuwar mutanen, yadda aka kama su da kuma yadda aka tsare su, tare da tantance ko akwai sakaci, laifi ko wata gudummawa daga jami’an hukumar.

Ministan ya kuma umurci NSCDC da sauran jami’an da abin ya shafa su ba kwamitin cikakken hadin kai, tare da kare dukkan bayanai da shaidu da suka shafi lamarin. Ya gargadi duk wanda ya yi ƙoƙarin ɓoye shaida ko hana binciken gudanar da aikinsa.

Mutanen 37 sun mutu ne bayan an kama su yayin samamen NSCDC kan masu haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a yankunan M.I. Wushishi da Lukoto na Jihar Neja a ranakun 15 da 16 ga Satumba. Kwamitin binciken na da makonni biyu domin gabatar da rahotonsa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments