Gwamnatin Jihar Sokoto ta kafa kwamiti mai mutum 14 domin binciken ce-ce-ku-ce da ya biyo bayan wasu kalamai da aka danganta da Malam Musa Lukuwa kan batutuwan shari’a.
Kwamishinan Harkokin Addini na jihar, Sheikh Dr Jabir Maihula, na cikin mambobin kwamitin, yayin da Barrister Gandi Umar Muhammad zai zama sakataren kwamitin.
Kwamitin, wanda Mallam Yahaya na Malam Boyi ke jagoranta, ya kunshi wakilan ƙungiyoyin Izala, Tijjaniyya, Ƙadiriyya, Jama’atu Nasril Islam da Majalisar Sultan.
Gwamna Ahmed Aliyu ya umurci kwamitin da ya duba matsayin shari’a kan batutuwan da Lukuwa ya gabatar, sannan ya bai wa gwamnati shawarwari bisa sakamakon bincikensa.
An bai wa kwamitin wa’adin kwanaki 14 domin gabatar da rahotonsa ga gwamnatin jihar.