Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiAn shafe sa’o’i 12 ana makale a a cunkoson ababen hawa a...

An shafe sa’o’i 12 ana makale a a cunkoson ababen hawa a titin Lagos-Ibadan

Masu ababen hawa da fasinjoji sun shafe sama da sa’o’i 12 a makale a titin Lagos-Ibadan, bayan wani haɗarin motoci bakwai a gadar Kara.

Masu ababen hawa da fasinjoji sun shafe sama da sa’o’i 12 a makale a titin Lagos-Ibadan, bayan wani haɗarin motoci bakwai a gadar Kara.

Cunkoson ya bazu daga Long Bridge zuwa Magboro har zuwa wasu sassan Lagos, inda wasu matafiya suka kwana a hanya.

LASEMA ta ce wata tirelar kwantena ta samu matsalar inji, ta rasa iko da ita sannan ta buge wasu motoci shida.

Jami’an LASTMA da ’yan sanda sun shiga aikin ceto tare da cire motocin da hatsarin ya rutsa da su daga hanya.

LASEMA ta ce babu wanda ya mutu ko ya samu rauni a hatsarin, yayin da jami’an LASTMA suka ci gaba da kokarin rage cunkoson.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments