Fitaccen jarumi a masana’antar fina-finai ta Najeriya, Ou Jacobs ya rasu.
Ɗansa, Olusoji Jacobs, ne ya sanar da rasuwar a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar Laraba.
Ya ce:
“Cikin godiya ga Allah bisa rayuwar da ta yi mai ma’ana da da kuma kalubale daban-daban, muna sanar da rasuwar mijinmu, uba, kakana da kawunmu ƙaunatacce.”
“Oludotun Baiyewun Jacobs (MFR). 11/07/1942 – 16/09/2026. Muna kira ga dukkan masu rubutu a yanar gizo da masu tasiri a kafafen sada zumunta da su mutunta sirrin iyalinmu a wannan lokaci.”
Olu Jacobs ya fara sana’ar wasan kwaikwayo ne ta hanyar fitowa a wasu shirye-shiryen talabijin na Birtaniya da fina-finai na ƙasa da ƙasa.
Ya halarci makarantar Holy Trinity, inda ya kasance mamba a ƙungiyoyin muhawara da wasan kwaikwayo na makarantar.
Jacobs ya samu ƙwarin gwiwar shiga harkar wasan kwaikwayo ne bayan da ya halarci ɗaya daga cikin bukukuwan wasan kwaikwayo na shekara-shekara na marigayi Cif Hubert Ogunde a Colonial Hotel da ke Kano.
Bayan haka, ya samu takardar izinin shiga Birtaniya, inda ya tafi domin karantar wasan kwaikwayo.
A Birtaniya, Jacobs ya yi karatun wasan kwaikwayo a The Royal Academy of Dramatic Arts da ke London.
Ɗ