Saturday, October 17, 2026
HomeWasanniMessi zai buga wasan bankwana da tawagar Argentina

Messi zai buga wasan bankwana da tawagar Argentina

Fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa, Lionel Messi, zai samu damar yin wasan bankwana da tawagar Argentina bayan an saka sunansa cikin jerin ‘yan wasan da za su fafata da Benin a wasan sada zumunci ranar 6 ga Oktoba, 2026.

Za a buga wasan ne a filin wasa na Monumental da ke Buenos Aires, inda ake sa ran zai zama wasan ƙarshe na Messi cikin rigar Argentina. Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Argentina, Claudio Tapia, ya tabbatar da cewa an gayyaci Messi domin a yi masa bankwana da ya dace da tarihin da ya yi da tawagar ƙasar.

Haka kuma, an gayyaci ‘yan wasan da suka lashe gasar Kofin Duniya ta 2022 tare da Messi domin su kasance cikin bikin bankwanan. Kafin wasan Benin, Argentina za ta kara da Bolivia a ranar 30 ga Satumba, sannan ta kara da Burkina Faso ranar 3 ga Oktoba.

Rahotanni sun bayyana cewa wasan Benin zai zama wasan Messi na 208 kuma na ƙarshe da tawagar Argentina, bayan shafe sama da shekaru 20 yana wakiltar ƙasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments