Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaTinubu kawai nake goyon baya a zaben 2027 – Nyesom Wike

Tinubu kawai nake goyon baya a zaben 2027 – Nyesom Wike

Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ce goyon bayan da yake bai wa Shugaba Bola Tinubu domin sake zaɓe a 2027 ba yana nufin zai hana jam’iyyar PDP shiga sauran zaɓukan da za a gudanar ba.

Wike ya bayyana cewa matsayinsa ya taƙaita ne kan goyon bayan Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa, yayin da PDP ke da cikakken ’yancin tsayar da ’yan takararta a zaɓukan gwamna, majalisar dokokin tarayya da majalisun dokokin jihohi.

Sanarwar da mai ba Wike shawara na musamman kan hulɗa da jama’a da kafafen sada zumunta, Lere Olayinka, ya fitar ranar Talata ce ta bayyana wannan matsaya, kamar yadda TVC ta ruwaito.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments