Rundunar Operation Hadin Kai ta ce dakarunta da ke yaƙi da Boko Haram da ISWAP a Arewa maso Gabashin Najeriya sun kashe mayakan ƙungiyoyin biyu 1,106 cikin shekara guda.
Kwamandan rundunar mai barin gado, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, ne ya bayyana hakan yayin bikin miƙa ragamar jagorancin rundunar ga Manjo Janar Ibikunle Ajose a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Ya ce a cikin wannan lokaci, sojojin sun ƙwato makamai sama da 475 da harsasai fiye da 24,000, tare da lalata bama-bamai 295 da aka ƙera a cikin gida.
Haka kuma, an kama mutane 758 da ake zargi da taimaka wa ’yan ta’adda wajen safarar makamai da sauran kayayyaki.
Manjo Janar Abubakar ya ƙara da cewa mayakan JAS da ISWAP 969 da iyalansu sun miƙa wuya, yayin da aka ceto fararen hula 638 daga sansanonin ’yan ta’adda.
A cewarsa, ayyukan sojojin sun kuma taimaka wajen mayar da iyalai sama da 7,000 da suka rasa matsugunansu zuwa garuruwansu a Borno.
Bugu da ƙari, rundunar ta ce a sake buɗe wasu kasuwanni da hanyoyin kasuwanci, tare da dawo da wasu ayyukan ilimi kamar jarrabawar WAEC da NECO a wasu yankuna.
An kuma ce an ƙwato Naira miliyan 300 da ake zargin suna da alaƙa da masu ɗaukar nauyin ta’addanci, tare da taimakawa wajen dawo da ’yan Nijeriya sama da 3,000 daga Kamaru.
Sabon kwamandan rundunar, Manjo Janar Ibikunle Ajose, ya yi alƙawarin ci gaba da ƙoƙarin da ake yi wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Arewa maso Gabas, tare da aiki tare da gwamnatin jiha, ƙungiyoyin agaji da sauran masu ruwa da tsaki.