Saturday, October 17, 2026
HomeFasahaKamfanin Apple ya ƙaddamar da iPhone mai ninkewa da kuma iPhone 18...

Kamfanin Apple ya ƙaddamar da iPhone mai ninkewa da kuma iPhone 18 Pro

Kamfanin Apple ya ƙaddamar da sabuwar iPhone Duo, wayarsu ta farko da ake ninkewa, a yayin taron ƙaddamar da sabbin kayayyakin kamfanin da aka gudanar a ranar Laraba. Wayar tana da allo mai girman inci 7.6 idan an buɗe ta da kuma wani allo mai inci 5.4 a wajen ta.

Kamfanin Apple ya ƙaddamar da sabuwar iPhone Duo, wayarsu ta farko da ake ninkewa, a yayin taron ƙaddamar da sabbin kayayyakin kamfanin da aka gudanar a ranar Laraba. Wayar tana da allo mai girman inci 7.6 idan an buɗe ta da kuma wani allo mai inci 5.4 a wajen ta.

iPhone Duo ɗin na da farashin da ke farawa daga dala $1,999, kuma ya ce tana amfani da guntu na A20 Pro, sabon tsarin sanyaya da kuma modem ɗin C2 da kamfanin ya ƙera. Wayar na kuma iya ɗaukar ma’ajiyar bayanai har zuwa 2TB, yayin da za a fara sayar da ita a ranar 23 ga Oktoba 2026.

Apple ta kuma gabatar da iPhone 18 Pro da 18 Pro Max, waɗanda farashinsu ya fara daga $1,199 da $1,299. Sabbin wayoyin sun samu ingantacciyar kyamara mai megapixel 48, da tsarin buɗe ruwan tabarau wanda ke taimakawa wajen ɗaukar hotuna a yanayi daban-daban.

Sabon Shugaban Kamfanin Apple, John Ternus, ya jagoranci taron na farko tun bayan da ya maye gurbin Tim Cook. Ya jaddada yadda kamfanin ke ƙara mayar da hankali kan fasahar basirar wucin gadi, musamman tsarin Siri da kuma sarrafa bayanan AI a cikin na’urar domin kare sirrin masu amfani.

Baya ga sabbin iPhone, Apple ta ƙaddamar da Apple Watch Series 12 da Apple Watch Ultra 4, tare da sabbin AirPods da suka fara daga $129. Shigowar Apple kasuwar wayoyin wadda ake ninkewa na ƙara bayyana tseren su da Samsung da Huawei, waɗanda suka dade suna kan gaba a wannan fanni.

SourceRouters
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments