Saturday, October 17, 2026
HomeLafiyaMutane 13 sun rasu sakamakon cutar mashako a jihar Yobe

Mutane 13 sun rasu sakamakon cutar mashako a jihar Yobe

Hukumomin lafiya sun ce adadin ya ragu sosai idan aka kwatanta da shekarun baya.

Jihar Yobe ta samu mutane 511 da suka kamu da cutar mashako wato ‘diphtheria’, yayin da mutane 13 suka mutu daga watan Janairu zuwa 8 ga Satumba, a cewar hukumomin lafiya.

Kwamishinan Lafiya da Ayyukan Jinƙai na jihar, Muhammad Gana, ne ya bayyana hakan a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Damaturu ranar Alhamis.

Muhammad Gana ya ce mutuwar mutane 13 ta yi daidai da kashi 2.5 cikin 100 na yawan masu cutar, wanda ya ce ya yi ƙasa da adadin mace-macen da aka samu a mafi yawan jihohin Najeriya da cutar ta shafa.

Ya tabbatar da cewa cutar ta bulla a ƙananan hukumomi 12 na jihar, inda ya ce shirye-shiryen gudanar da allurar rigakafi a yankunan ke ci gaba sosai.

Kwamishinan ya ƙara da cewa adadin mutane 511 da aka samu da cutar a halin yanzu ya yi ƙasa sosai idan aka kwatanta da mutum 1,100 da aka samu da cutar a watan Satumban 2025 da kuma shekarun baya.

Ya danganta raguwar cutar tun daga shekarar 2023, lokacin da jihar ta samu mafi yawan masu cutar har mutum 3,080, da ci gaba da gudanar da ayyukan yaƙi da annobar.

Daga cikin matakan da gwamnatin jihar ta ɗauka akwai samar da magunguna kyauta ga masu cutar, horas da ma’aikatan lafiya kan hanyoyin tunkarar annobar, gudanar da allurar rigakafi a yankunan da ke da wahalar isa, da kuma wayar da kan al’umma game da cutar.

Sauran matakan sun haɗa da gano mutanen da suka yi hulɗa da masu cutar cikin gaggawa, raba bayanai da masu ruwa da tsaki, gudanar da tarukan haɗin gwiwa akai-akai da kuma tattara kayan aiki da kuɗaɗen da ake buƙata domin tunkarar annobar.

Gana ya yaba da tallafin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), UNICEF da African Field Epidemiology Network (AFENET), musamman wajen taimaka wa jihar wajen gudanar da allurar rigakafin cutar a tsakanin al’ummomin makiyaya.

Mashako cuta ce da ƙwayoyin cuta ke haddasawa, wadda ta fi shafar maƙogwaro da hanyoyin numfashi na sama.

Cutar tana yaɗuwa musamman ta ɗigon ruwa da ke fita daga baki ko hancin mutum yayin tari ko atishawa. Haka kuma, tana iya yaɗuwa ta hanyar taɓa raunukan fata na mai cutar kai tsaye ko kuma taɓa abubuwan da suka gurɓata da ruwan jiki daga mai cutar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments