Saturday, October 17, 2026
HomeTsaro'Yan sanda sun dakile harin ta’addanci kan ayarin ɗan takarar APC a...

‘Yan sanda sun dakile harin ta’addanci kan ayarin ɗan takarar APC a Borno

An tabbatar da cewa babu wanda ya ji rauni a harin

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta ce jami’an rundunar sun dakile wani harin da ’yan ta’adda suka kai kan ayarin motocin Mustapha Gubio, ɗan takarar gwamnan Jihar Borno na jam’iyyar APC, tare da wasu manyan ’yan siyasa.

Harin ya faru ne a ranar Alhamis a hanyar Kareto zuwa Damasak da ke Jihar Borno.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Juma’a, ta ce ’yan ta’addan sun kai wa ayarin hari da bama-bamai da aka ƙera da kansu (IEDs) da kuma rokoki masu linzami (RPGs).

Sai dai jami’an tsaron da ke cikin ayarin sun mayar da martani, inda suka tilasta wa maharan tserewa zuwa cikin daji.

Bayan haka, jami’an sun binciki tare da duba hanyar domin tabbatar da cewa babu wasu bama-bamai da aka sake dasawa, kafin a kai ayarin zuwa wani wuri mai tsaro.

Sanarwar rundunar ta ce, “Tawagar dabarun yaƙi ta tilasta wa ’yan ta’addan komawa cikin dajin da ke kewaye, sannan ta binciki tare da duba yankin domin kawar da barazanar wasu bama-bamai.”

Rundunar ta kuma ce babu wanda ya ji rauni ko ya rasa ransa a cikin ayarin.

Ta ƙara da cewa, “An kwashe ayarin da ke ɗauke da ɗan takarar gwamna, jami’an gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki zuwa wani wuri mai aminci, ba tare da an samu asarar rai ko wani rauni ga mutanen da ke cikinsa ba.”

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments