Fadar Shugaban Ƙasar Najeriya ta ce shari’ar da ake yi a wata Kotun Tarayya da ke Washington, D.C., a Amurka ba shari’ar laifi ba ce da ake yi kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Fadar ta ce shari’ar ta shafi wata takaddama ce kan buƙatar bayyana wasu bayanan da hukumomin Amurka ke riƙe da su, ƙarƙashin dokar Freedom of Information Act (FOIA).
A cikin wata sanarwa da mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Alhamis, an bayyana cewa hukumomin FBI da DEA sun riga sun gabatar da shafuka 399 na bayanan da suka shafi batun.
Sai dai sanarwar ta ce an cire ko ɓoye wasu sassan bayanan ne bisa tanade-tanaden dokar Amurka, abin da ya sa yanzu takaddamar ta fi karkata kan ko dalilan da hukumomin suka bayar na ɓoye bayanan sun yi daidai da abin da doka ta tanada.
Fadar Shugaban Ƙasar ta jaddada cewa bayyana bayanai ko kuma hana bayyana su ba ya zama hujjar cewa an aikata wani laifi ba.
Ta kuma yi kira ga kafafen yaɗa labarai da jama’a da su bambanta tsakanin sahihin tsarin shari’a da kuma zarge-zargen siyasa ko jita-jitar da ba su da ingantaccen tushe.
Sanarwar ta ce ya kamata a fahimci batun bisa tsarin shari’a da dokokin Amurka da ke jagorantar yadda hukumomin gwamnati ke bayyana bayanan da suke riƙe da su.