Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta wallafa jerin sunayen ’yan takarar gwamna da za su fafata a zaɓen 2027 a jihohin Najeriya.
Sai dai jerin sunayen ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin ’yan siyasa, musamman bayan da wasu ’yan takarar da suka lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyunsu suka kasa ganin sunayensu cikin jerin da hukumar ta wallafa.
A wasu jihohi, an sauya sunayen ’yan takara tare da maye gurbinsu da wasu mutane.
A Adamawa, misali, an sauya sunayen Ambasada Omar Suleiman, wanda aka fi sani da Omarana, na jam’iyyar ADC, da Caleb Andrew na PDP. An maye gurbin ɗan takarar ADC da Hamman Tukur Modibbo Ribadu.
A Neja, ɗan takarar gwamna na PDP, Abubakar Suleiman, ya amince da janyewa daga takarar.
A Nasarawa kuma, sunayen tsohon Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Mohammed Abubakar Adamu, da Sanatan Nasarawa ta Kudu, Mohammed Ogoshi Onawo, ba su bayyana cikin jerin ba.
Maimakon haka, INEC ta sanya Musa Adamu Angba a matsayin ɗan takarar SDP, yayin da Mohammed Awwal Suleiman ya bayyana a matsayin ɗan takarar APM.
Angba ya ce a shirye yake ya miƙa tikitin SDP ga tsohon IGP Mohammed Adamu idan hakan ya zama dole, yana mai cewa yana da kyakkyawar alaƙa da shi.
Sai dai ya musanta cewa ya riga ya amince da wata yarjejeniya ta janyewa, bayan wasu bayanai sun fara yaɗuwa a kafafen sada zumunta.
A halin yanzu dai sauye-sauyen sunayen da aka gani a jerin INEC sun jawo hankalin ’yan takara da magoya bayansu, inda wasu suka fara zuwa ofisoshin hukumar domin neman ƙarin bayani.