Sanata Rufai Sani Hanga, mai wakiltar mazabar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, ya bayyana dalilin da ya sa dangantakarsa da tsohon Gwamnan Kano kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ta yi tsami.
Hanga ya ce rashin fahimtar juna kan shirye-shiryen tallafa wa jama’a da kuma harkokin siyasa ne suka jawo matsala tsakaninsa da Kwankwaso.
A wata hira da Dan’uwa Rano TV, Sanatan ya ce Kwankwaso ya fusata bayan da ya shirya wani babban shirin tallafa wa al’ummar mazabarsa.
Hanga ya ce a yayin shirin, ya raba motoci, shinkafa, takin zamani, injinan nika, dabbobi da sauran kayayyaki ga jama’a.
Ya ce rashin jituwar ta kara kamari ne saboda an gudanar da taron a wani wuri da ke da alaka da Kwankwaso, wanda tun farko ya amince zai halarci taron.
A cewar Hanga, wurin taron ya cika da motoci, buhunan shinkafa, takin zamani, dabbobi da sauran kayayyakin tallafin. Ya ce an kwashe kusan kwana daya da rabi ana jigilar kayayyakin zuwa wurin.
Hanga ya tuna cewa Kwankwaso ya nuna rashin jin dadinsa bayan da ya isa wurin taron.
Ya ce tsohon gwamnan ya bukaci wadanda ke wurin su dakata domin yin sallah, sannan ya bar wurin amma bai sake dawowa ba.
Sanatan ya ce an ci gaba da rabon kayayyakin a gaban wasu manyan ‘yan siyasa, ciki har da tsohon Mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, Wada Sagagi, Batayya, Nasiru Gawuna da wasu mambobin Majalisar Dokoki ta Tarayya.
Hanga ya ce daga baya Kwankwaso ya yi masa magana kan taron, inda ya zarge shi da shirya rabon kayayyakin ne domin jama’a su yaba masa kan irin nasarar da ya samu a matsayin sanatan Kano ta Tsakiya.
“Ya ce, ‘Ka zo kana rabawa (tallafi) saboda mutane suna yaba maka, suna cewa Kano ta Tsakiya ba ta taba samun Sanata irinka ba. Ba za ka iya kawo kayayyakin nan wurinmu mu raba ba. Ka ba ni buhunan shinkafa 50, buhunan takin zamani 50 da shanu uku. Ina jin yunwa ne, ko ba ni da su? Shi ya sa na ki dawowa bayan sallah,’” in ji Hanga yana ambaton abin da Kwankwaso ya fada masa.
Sanatan ya ce ya nemi afuwa tare da yin alkawarin warware duk wata rashin fahimta da ta shiga tsakaninsu.
Sai dai Hanga ya ce a baya Kwankwaso ya taba tura mutane domin neman a sanya wasu mutane cikin wadanda za su amfana da shirye-shiryen tallafin nasa.
Ya kuma yi zargin cewa Kwankwaso ya tura Sunusi Surajo Kwankwaso domin ya nemi ya samar da mota ga wani wanda zai amfana daga Shanono, wadda ba ta cikin mazabar Kano ta Tsakiya.
Hanga ya ce daga karshe ya sayi motar bayan an sanar da shi cewa motar wanda aka tanadar wa tallafin ta samu matsala sakamakon hatsari a lokacin yakin neman zaben Kwankwaso.
“Na gaya masa cewa duk wanda yake son mu taimaka masa, a shirye muke mu taimaka,” in ji Hanga.
Ya ce wannan lamari ya sa ya fahimci cewa mutuncin juna da ya kasance a tsakaninsa da Kwankwaso ya fara gushewa.
“A nan ne na fahimci cewa rashin girmamawa ya fara shiga. Ya taba yi wa wasu irin wannan, amma bai taba yi min ba sai a wannan lokacin. Sai na ce wa kaina, tunda ya fara yin haka a kaina, alama ce ta rashin girmamawa kuma abubuwa ba za su kare lafiya a tsakaninmu ba,” in ji shi.
Hanga ya kara da cewa Kwankwaso bai ji dadin girman shirye-shiryen tallafa wa jama’a da yake gudanarwa ba, da kuma yadda shahararsa ke kara karuwa a tsakanin jama’a.
Sanatan ya kuma danganta rashin samun damar sake tsayawa takara da jam’iyyar da kuma tabarbarewar dangantakarsa da Kwankwaso, wanda ya kira “Jagora” na tafiyar.