An kama wata mata bisa zargin ƙoƙarin shigar da wasu abubuwan da ake zargin miyagun ƙwayoyi ne cikin Cibiyar Gyaran Halayen Fursunoni ta Matsakaicin Tsaro da ke Ibara, Abeokuta, Jihar Ogun.
An bayyana matar da sunanta Mrs Iyabo Sowunmi, wadda aka kama ranar Juma’a yayin gudanar da binciken tsaro na yau da kullum a babbar ƙofar gidan yarin.
Rahotanni sun ce jami’an tsaro sun gano wani abu da ake zargi da miyagun ƙwayoyi ne, wanda aka ɓoye cikin leda mai ɗauke da garin Milo.
Ana zargin abun da aka gano da kasancewa “Colos”, wani nau’in ƙwayar sinadarai da ke shafar kwakwalwa.
Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya (NCoS) da ke Jihar Ogun ta tabbatar da kama matar a ranar Litinin.
Mai magana da yawun hukumar a jihar, Odukoya Olayinka, ya ce ana zargin Sowunmi tana ƙoƙarin kai kunshin ga wani fursuna mai suna Dare Sowunmi, wanda ke fuskantar hukuncin kisa.
Olayinka ya kuma tabbatar da cewa matar ita ce mahaifiyar fursunan.
“Da misalin ƙarfe 1:33 na rana ranar Juma’a, 28 ga Agusta, 2026, yayin gudanar da binciken tsaro na yau da kullum a babbar ƙofar cibiyar, an gano wasu abubuwa da ake kyautata zaton ƙwayar sinadarai ce da aka fi sani da ‘Colos’, waɗanda aka ɓoye cikin leda mai ɗauke da garin wani shahararren abin sha.
Olayinka ya ce bayan gano abin, jami’an hukumar sun tsare Mrs Sowunmi, daga bisani kuma suka miƙa ta ga Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) domin gudanar da bincike da kuma gurfanar da ita a gaban kotu.
Kwanturolan Hukumar Gyaran Hali a Jihar Ogun, Abioye Kamoru Adesina, ya yaba wa jami’an tsaron bisa kaifin basirarsu da kuma bin ƙa’idojin tsaro.
“An kafa cibiyoyin tsare masu laifi ne domin tabbatar da tsaron jama’a, gyara halaye da kuma taimaka wa waɗanda aka tsare wajen komawa cikin al’umma. Ba za mu lamunci safarar miyagun ƙwayoyi ko duk wani abu na haram da zai iya kawo cikas ga tsaro,” in ji Adesina.
Olayinka ya kuma yi kira ga jama’a da su mutunta cibiyoyin tsare masu laifi, tare da gargaɗin cewa duk wanda ya yi ƙoƙarin lalata ko kawo cikas ga tsaron gidan yari zai fuskanci cikakken hukuncin doka.