Matatar Dangote ta yi gargadin cewa za ta iya kara fitar da rarar man fetur da take da shi zuwa kasuwannin kasashen waje, sakamakon karuwar shigo da fetur daga ketare zuwa Najeriya.
Kamfanin ya ce yawan man fetur da ake shigowa da shi kasar na haifar da rashin tabbas wajen hasashen bukatar kasuwar cikin gida da kuma tsara adadin man da ya kamata ta samar da kuma adana.
A cewar matatar, man fetur da aka shigo da shi daga kasashen waje ya kai kusan kashi 43 cikin 100 na jimillar fetur da aka samar wa kasuwar Najeriya a watan Yuli, duk da cewa matatar tana da karfin samar da man da zai iya biyan bukatar cikin gida.
Matatar ta bayyana cewa ci gaba da bayar da lasisin shigo da fetur na kara mata wahala wajen tsara samarwa da kuma kula da ajiyar man da take da shi.
Ta ce idan ba a samu kasuwar cikin gida da za ta dauki rarar man da aka samar ba, dole ne a fitar da shi zuwa kasuwannin yankin da sauran kasashen duniya domin kauce wa karin kudaden ajiya da na hada-hadar kudi.
Dangote ta jaddada cewa kara fitar da man zuwa kasashen waje ba yana nufin ta kasa biyan bukatar Najeriya ba ne, sai dai matakin martani ne ga rarar man da rashin tabbas da shigo da fetur daga ketare ke haifarwa.
Matatar ta kuma yi kira da a kara gaskiya da mu’amala mak kyau kan yawan man da ake shigowa da shi, tare da samar da manufofin da za su karfafa matatun cikin gida da rage dogaro da man fetur daga kasashen waje.