Jami’an tsaro sun fatattaki wasu ’yan bindiga da suka yi yunkurin kai hari kauyen Sifawa da ke karamar hukumar Bodinga a Jihar Sokoto.
Rahotanni sun ce maharan sun kai harin ne da safiyar Laraba, inda suka yi kokarin mamaye barikin sojoji da ke yankin.
Sai dai sojoji da ’yan sanda da ke bakin aiki sun yi artabu da su na tsawon sa’o’i kafin jami’an tsaron suka samu nasarar fatattakarsu.
An ce sojoji biyu sun samu raunuka a yayin musayar wutar, kuma an garzaya da su asibiti domin kula da lafiyarsu.
Majiyoyi sun bayyana cewa an kashe wasu daga cikin ’yan bindigar yayin arangamar, yayin da wasu suka tsere zuwa cikin gonaki da dazuzzukan yankin.
Rahotanni sun kuma ce an fara kai hare-haren sama kan wuraren da ake zargin ’yan bindigar da suka tsere sun fake, yayin da jami’an tsaro ke shirin ci gaba da farmakin domin kamo sauran.