Saturday, October 17, 2026
HomeTsaro’Yan bindiga sun hallaka mutum 4, sun jikkata 7 tare da yin...

’Yan bindiga sun hallaka mutum 4, sun jikkata 7 tare da yin garkuwa da wasu a Sokoto

Wasu ’yan bindiga sun kai hari ƙauyen Gorau da ke ƙaramar hukumar Goronyo a Jihar Sokoto, inda suka kashe mutane huɗu tare da yin garkuwa da wasu huɗu.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9 na dare ranar Laraba, kwanaki shida kacal bayan wani hatsarin kwale-kwale da ya afku a yankin, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 65.

A yayin harin, maharan sun kuma harbe wasu mazauna ƙauyen bakwai, waɗanda suka samu raunuka kuma a halin yanzu suke karɓar magani a asibiti.

Rahotanni sun ce ’yan bindigar sun fi mayar da hankali ne kan iyalan mutanen da suka rasa ’yan uwansu a hatsarin kwale-kwalen.

Ana zargin maharan sun kai harin ne domin karɓar kuɗin da Gwamnatin Jihar Sokoto ta yi alkawarin bai wa iyalan waɗanda suka mutu a hatsarin, inda ta ware Naira miliyan ɗaya ga kowane iyali.

Harin ya ƙara jefa mazauna yankin cikin fargaba, musamman bayan mummunan hatsarin kwale-kwalen da ya yi sanadin asarar rayuka da dama.

Ƙarin bayani na nan tafe.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments