Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC a zaɓen 2027, Peter Obi, ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu shugabannin addini ke yi wa wasu ’yan siyasa addu’a da neman musu albarka, duk da zargin da ake yi musu na aikata laifuka.
Obi ya ce irin wannan hali na daga cikin abubuwan da ke nuna irin ƙalubalen da tsarin mulki da al’umma ke fuskanta a Najeriya.
Tsohon gwamnan Jihar Anambra ya bayyana hakan ne yayin wani taron Goodluck Jonathan Foundation Democracy Dialogue 2026, da aka gudanar a Bauchi.
A yayin taron, Obi ya kuma nuna damuwa kan yadda tsarin shari’a da na zaɓe ke tafiya a ƙasar, yana mai cewa ana samun koma baya wajen mutunta ƙa’idoji da tsarin dimokuraɗiyya.
Obi ya bayyana cewa ya taɓa shafe tsawon shekaru uku yana kalubalantar sakamakon wani zaɓe a gaban kotu, inda alkalai biyar da bai taɓa sani ko haɗuwa da su ba suka yanke hukunci kan ƙarar tasa.
Ya kuma yi zargin cewa wasu sauye-sauyen da aka samu a dokokin zaɓe sun raunana wasu matakai da ya kamata su taimaka wajen tabbatar da gaskiya da adalci a lokacin zaɓe.
A cewarsa, akwai buƙatar dakatar da duk wani abu da zai ƙara raunana tsarin dimokuraɗiyya, domin tabbatar da cewa al’umma da tsararraki masu zuwa sun gaji ƙasa mai ingantattun cibiyoyi da tsarin shugabanci.
Obi ya jaddada cewa mutunta doka, inganta tsarin shari’a da kuma tabbatar da sahihin zaɓe na daga cikin muhimman abubuwan da za su taimaka wajen sake gina Najeriya.