Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiHukumar kare haƙƙin dan adam ta buƙaci a kama Sheikh Jingir

Hukumar kare haƙƙin dan adam ta buƙaci a kama Sheikh Jingir

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta Najeriya ta yi Allah wadai da wasu kalaman da fitaccen malamin addini, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya yi, tana mai cewa kalaman na iya ƙara rura wutar ƙiyayya da rarrabuwar kawuna tsakanin mabiya addinai.

Hukumar ta buƙaci Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Hukumar DSS da sauran hukumomin tsaro da abin ya shafa da su gudanar da bincike tare da kama Sheikh Jingir, sannan a gurfanar da shi bisa zargin furta kalaman da ka iya tunzura jama’a.

Shugaban Hukumar, Tony Ojukwu, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa, inda ya ce kalaman malamin da aka yada a wani faifan bidiyo sun ƙunshi abin da ya bayyana a matsayin kira ga nuna wariya ga mabiya wasu addinai, ciki har da amfani da kalmar “kafirai”.

A cewar hukumar, irin waɗannan kalamai na iya sabawa ƙa’idojin da suka shafi daidaito, mutunta juna da zaman lafiya tsakanin ’yan Najeriya, tare da ƙara haɗarin barkewar rikici.

Hukumar ta kuma yi kira ga malaman addini, sarakuna da ’yan siyasa da su guji duk wani furuci da zai iya raba kan al’umma ko ƙara haifar da rashin jituwa tsakanin mabiya addinai.

Ta ce za ta ci gaba da sa ido kan abubuwan da ka iya shafar zaman lafiya da haƙƙin ɗan Adam yayin da ƙasar ke tunkarar zaɓen 2027.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta Najeriya ta buƙaci hukumomin tsaro su kama tare da gurfanar da Sheikh Sani Yahaya Jingir kan zargin kalaman ƙiyayya da tunzura jama’a.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments