An shiga jimami a harkar ƙwallon ƙafa ta Najeriya bayan rasuwar ɗan wasan Katsina United, Uzor, yayin wani wasan sada zumunci da ƙungiyar ta fafata da Niger Tornadoes.
Lamarin ya faru ne a filin wasa na Muhammadu Dikko Stadium da ke Katsina, yayin da wasan ke dab da ƙarewa. Rahotanni sun ce Uzor ya fadi a lokacin fafatawar, lamarin da ya sa aka garzaya da shi asibiti domin samun kulawar gaggawa.
Sai dai duk da ƙoƙarin ceto rayuwarsa, daga bisani aka tabbatar da rasuwar ɗan wasan, abin da ya jefa ’yan wasa da magoya bayan ƙungiyar cikin jimami.
Uzor ya koma Katsina United ne daga Kano Pillars, inda ya kasance cikin ’yan wasan da suka taka leda a ƙungiyar. Rasuwarsa ta ƙara jefa al’ummar ƙwallon ƙafa cikin alhini.
Ana sa ran ƙungiyar Katsina United da sauran masu ruwa da tsaki a harkar ƙwallon ƙafa za su bayyana ƙarin bayani kan rasuwar ɗan wasan da kuma shirye-shiryen jana’izarsa.