Saturday, October 17, 2026
HomeIlimiMasarautar Kano ta karyata jita-jitar cewa Sanusi II ya samu ‘carry-over‘ a...

Masarautar Kano ta karyata jita-jitar cewa Sanusi II ya samu ‘carry-over‘ a jami’a

Majalisar Masarautar Kano ta musanta wani rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke ikirarin cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya samu ‘carry-over’ a ɗaya daga cikin darussan da yake karantawa a fannin Shari’a a Jami’ar Northwest da ke Kano.

Sakataren Ofishin Sarkin, Muhammad Ado, ya bayyana cewa rahoton ba shi da tushe, yana mai cewa Sarkin na ci gaba da karatunsa cikin nasara kuma yana kan hanyar kammala shi da First Class, inda maki ɗaya kacal ya rage masa.

Haka kuma, wani ɗalibin jami’ar, Ibrahim Abubakar-Danmasani, ya bayyana cewa har zuwa ranar Lahadi ba a fara jarabawar jami’ar ba, inda aka tsara fara jarabawar ranar Litinin.

Wata majiya daga jami’ar ta kuma bayyana cewa bidiyon da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta ba ya nuna ainihin halin da karatun Sarkin ke ciki.

A cewar majiyar, wasu matasa ne suka ɗauki bidiyon a matsayin wasa, daga bisani kuma aka yaɗa shi a kafafen sada zumunta, lamarin da ya haifar da jita-jitar cewa Sarkin ya fadi wani darasi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments