Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga malaman addini a Najeriya da sauran ƙasashen Afirka da su ƙara amfani da tasirinsu wajen yaƙi da ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma duk wani yunƙuri na amfani da addini wajen haifar da rikici.
Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Lahadi a Kano, cikin saƙon da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya isar a madadinsa yayin babban Mauludin Shehu Ahmad Al-Tijani (RTA).
Shugaban ya ce malaman addini na da muhimmiyar rawa wajen wayar da kan matasa game da illolin ta’addanci, da kuma koyar da zaman lafiya, haƙuri da kyawawan ɗabi’u.
Ya kuma yi kira ga shugabannin siyasa da su gudanar da mulki cikin adalci, tausayi da kishin al’umma domin ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.
Tinubu ya bayyana Najeriya a matsayin ƙasa mai muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin, yana mai cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da haɗin gwiwa da malaman addini da sarakunan gargajiya wajen inganta zaman lafiya, haɗin kai da mutunta juna.