Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiZa mu taimakawa Benin da sojoji don daƙile juyin mulki - ECOWAS

Za mu taimakawa Benin da sojoji don daƙile juyin mulki – ECOWAS

Ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS) ta ce a shirye take ta taimaka wa Jamhuriyar Benin da sojoji domin daƙile juyin mulkin da wasu sojoji suka yi iƙirarin yi.

Matakin na ECOWAS na zuwa ne bayan wani rukunin sojoji ya sanar da kifar da gwamnatin Shugaba Patrice Talon a kafar talabijin ɗin ƙasar a yau Lahadi tare da kafa gwamnatin riƙon ƙwarya.

Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ta ce ta ɗora wa sojojin alhakin “duk wani rai da aka rasa” sakamakon yunƙurin nasu.

“ECOWAS za ta taimaka wa gwamnati da al’umma da duk abin da ya kamata, ciki har da aika dakarun ko-ta-kwana domin kare tsarin mulki da kuma ‘yancin Benin,” a cewar sanarwar da hukumar Ecowas mai hedikwata a Abuja ta fitar

Sai dai hukumomi a ƙasar sun ce sun shawo kan lamurra bayan yunƙurin juyin mulkin.

“An shawo kan lamarin. Mafi yawan rundunar soja na goya wa shugaban ƙasa baya – kuma muna ƙara shawo kan al’amuran,” kamar yadda Ministan Harkokin Waje Shegun Adjadi Bakari ya faɗa wa kamfanin labarai na Reuters.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments