Sama da gidaje 100,000 ne suka ruguje a lokacin da wata mahaukaciyar guguwar ta taso daga mashigin Malaca a makon da ya gabata, wanda ya janyo mamakon ruwan sama da zabtarewar ƙasa a sassan ƙasar da ke kudu maso gabashin Asiya.
Ana ci gaba da ƙoƙarin kai ɗaukin ga mutane a yankunan da hanyoyi suka lalace, inda ake jefo kayan agaji daga jiragen sama a wasu wuraren.
Ambaliyar ruwan ta Indonesia na ɗaya daga cikin mumunan bala’o’i masu nasaba da yanayi da suka afkawa nahiyar Asiya a cikin ƴan makonnin nan, inda adadin waɗanda suka mutu a Sri Lanka da Thailand da Malaysia da Vietnam ya kusan 2,000.
Kafofin yaɗa labaran Indonesia sun ce an sako fursunonin daga wani gidan yari a lokacin da ambaliyar ruwa ta yi barazanar mamaye ginin, inda jami’ai suka ce babu inda za a aika da su.
An kuma samu rahotannin sace-sace a manyan kantuna a wasu wuraren.