Rahotanni sun ce jirgin ya rikito ne a kusa da sansanin sojan sama da ke Kainji jim kaɗan bayan tashinsa a ranar Asabar.
Mai magana da yawun rundunar sojan sama ta Najeriya, Ehimen Ejodame, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa, inda rundunar ta ce matuƙa jigrin “sun nuna bajinta”.
“Sun yi nasarar kawar da jirgin daga kan gidajen al’umma cikin ƙwarewa kafin su fice daga ciki,” a cewarsa.