Matakin na ECOWAS na zuwa ne bayan wani rukunin sojoji ya sanar da kifar da gwamnatin Shugaba Patrice Talon a kafar talabijin ɗin ƙasar a yau Lahadi tare da kafa gwamnatin riƙon ƙwarya.
Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ta ce ta ɗora wa sojojin alhakin “duk wani rai da aka rasa” sakamakon yunƙurin nasu.
“ECOWAS za ta taimaka wa gwamnati da al’umma da duk abin da ya kamata, ciki har da aika dakarun ko-ta-kwana domin kare tsarin mulki da kuma ‘yancin Benin,” a cewar sanarwar da hukumar Ecowas mai hedikwata a Abuja ta fitar
Sai dai hukumomi a ƙasar sun ce sun shawo kan lamurra bayan yunƙurin juyin mulkin.
“An shawo kan lamarin. Mafi yawan rundunar soja na goya wa shugaban ƙasa baya – kuma muna ƙara shawo kan al’amuran,” kamar yadda Ministan Harkokin Waje Shegun Adjadi Bakari ya faɗa wa kamfanin labarai na Reuters.