Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiJirgin sojin saman Najeriya ya rikito a jihar Neja

Jirgin sojin saman Najeriya ya rikito a jihar Neja

Matuƙa jirgin yaƙi na sojan Najeriya sun tsira da rayukansu bayan hatsarin da jirgin nasu ya yi a jihar Neja.

Rahotanni sun ce jirgin ya rikito ne a kusa da sansanin sojan sama da ke Kainji jim kaɗan bayan tashinsa a ranar Asabar.

Mai magana da yawun rundunar sojan sama ta Najeriya, Ehimen Ejodame, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa, inda rundunar ta ce matuƙa jigrin “sun nuna bajinta”.

“Sun yi nasarar kawar da jirgin daga kan gidajen al’umma cikin ƙwarewa kafin su fice daga ciki,” a cewarsa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments