Monday, October 19, 2026
HomeKasashen wajeYan majalisar Amurka sun isa Najeriya don binciken zargin kisan Kiristoci

Yan majalisar Amurka sun isa Najeriya don binciken zargin kisan Kiristoci

Tawagar 'yan majalissar Amurka ta sauka a Najeriya a yau Lahadi domin binciken gaskiyar iƙirarin yi wa Kiristoci kisan gilla

Nuhu Ribadu, mai ba shugaban Najeriya shawara kan tsaro, ya ce ya gana da wakilan kuma zuwan tawagar na cikin abubuwan da suka amince da shi.

“Tawagar ta ƙunshi ‘yan majalissar wakilai Mario Díaz-Balart, Norma Torres, Scott Franklin, Juan Ciscomani, da Riley M. Moore,” a cewar Ribadu cikin wata sanarwa a shafinsa na sada zumunta.

Kazalika, Jakadan Amurka a Najeriya Richard Mills na cikin tawagar.

Ribadu ya ce sun tattauna matakan yaƙi da ta’addanaci, da zaman lafiya a Afrika, da hanyoyin ƙarfafa ƙawancen tsaro tsakanin Najeriya da Amurka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments