Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da kashe kimanin Naira tiriliyan 2.078 domin aiwatar da manyan ayyukan gine-gine da gyaran hanyoyi a jihohi 10 na Najeriya.
Ministan Ayyuka, Injiniya David Umahi, ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na inganta ababen more rayuwa da bunƙasa tattalin arziki.
Ayyukan sun haɗa da gina sabbin hanyoyi da gyaran manyan tituna a jihohin Adamawa, Taraba, Ebonyi, Kwara, Cross River, Kogi, Legas, Neja, Oyo da Filato. A cewar Umahi, ayyukan za su taimaka wajen sauƙaƙa zirga-zirgar mutane da kayayyaki tare da inganta harkokin kasuwanci a faɗin ƙasar.
Haka kuma, FEC ta amince da ƙarin Naira biliyan 15 domin ci gaba da aikin titin Gashua a jihar Yobe, tare da ware Naira biliyan 15.246 don fara kashi na biyu na aikin titin Yola–Fufore–Gurin.
Shugaba Tinubu ya kuma umarci ma’aikatar ayyuka da ta fara shirin sake gina hanyoyin da suka lalace domin ƙara musu ɗorewa da inganta tsaro.