An gudanar da wankin cikin ɗakin Ka’aba na shekarar 1448H/2026 a ranar Talata, 15 ga watan Muharram, daidai da 30 ga watan Yuni, a birnin Makka na ƙasar Saudiyya.
Mataimakin Gwamnan Yankin Makka, Yarima Saud bin Mishal bin Abdulaziz, ne ya jagoranci bikin a madadin Sarkin Saudiyya, Salman bin Abdulaziz Al Saud.
Wanke cikin ɗakin Ka’aba na daga cikin al’adun da Masarautar Saudiyya ke gudanarwa a kowace shekara domin girmama wuri mafi tsarki a addinin Musulunci. A yayin bikin, ana amfani da ruwan Zamzam da aka gauraya da turare masu ƙamshi wajen tsaftace bangon cikin Ka’abar.
Bikin ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, malaman addini da masu kula da harkokin Masallacin Harami, inda suka gudanar da addu’o’i tare da roƙon Allah ya karɓi ibadu da kuma tabbatar da zaman lafiya ga al’ummar Musulmi.
Ka’aba ita ce alkiblar Musulmi a faɗin duniya, kuma wankinta na shekara-shekara na daga cikin muhimman al’adu da ke nuna daraja da tsarkin wannan wuri mai alfarma.