Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiKungiyar Miyetti Allah ta bukaci a saki shugabanta Bello Bodejo

Kungiyar Miyetti Allah ta bukaci a saki shugabanta Bello Bodejo

Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah ta yi kira ga gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro da su saki shugabanta na ƙasa, Alhaji Abdullahi Bello Bodejo, wanda ke tsare bisa zargin da ya shafi harkokin kuɗi.

Shugaban kungiyar na shiyyar Arewa maso Gabas, Alhaji Nasiru Liman Jalbu, ya ce mambobin kungiyar na roƙon Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Ministan Shari’a da sauran hukumomin da abin ya shafa su tabbatar an yi wa Bodejo adalci tare da ba shi damar kare kansa a gaban doka.

Kungiyar ta bayyana cewa an taba kama Bodejo a shekarar 2024 kan batun kafa ƙungiyar sintirin makiyaya, amma daga bisani aka sake shi bayan an janye tuhume-tuhumen da ake masa.

Ta ce an sake kama shi a watan Mayun 2026 bayan ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Sanatan Taraba ta Tsakiya a ƙarƙashin jam’iyyar APC a zaɓen 2027, inda ta buƙaci hukumomi su gudanar da shari’ar cikin gaskiya da adalci.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments