Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi iƙirarin cewa sojojin Amurka sun kawo ƙarshen kashe-kashen Kiristoci a Najeriya ta hanyar matakan soji da gwamnatin sa ta ɗauka kan ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya.
Trump ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin wani taro a birnin Washington, inda ya yi magana kan nasarorin gwamnatinsa wajen yaƙi da ta’addanci a sassa daban-daban na duniya.
A cewarsa, matakin da Amurka ta ɗauka a Najeriya ya taka muhimmiyar rawa wajen dakatar da hare-haren da ake zargin ana kai wa al’ummomin Kiristoci, musamman a yankunan da ke fama da matsalar ta’addanci.
Ya ce kafin wannan mataki, dubban mutane da suka haɗa da mata, yara da tsofaffi sun rasa rayukansu a munanan hare-hare.
Trump ya kuma yi iƙirarin cewa farmakin da sojojin Amurka suka kai ya raunana ƙungiyoyin da ke da hannu a hare-haren, inda ya ce an kashe shugabansu da mataimakansa, lamarin da ya sa sauran mayaƙan suka ja da baya saboda tsoron ƙarin hare-hare.