Cibiyar Centre for Reform and Public Advocacy (CFRPA) ta shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke Kano, tana neman a hana Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Ƙungiyar ta ce buƙatar ta ta samo asali ne daga zargin cewa shugaban ya gabatar da takardun shaidar karatu na bogi.