Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeSojojin Amurka sun kawo ƙarshen kashe-kashen Kiristoci a Najeriya – Donald Trump

Sojojin Amurka sun kawo ƙarshen kashe-kashen Kiristoci a Najeriya – Donald Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi iƙirarin cewa sojojin Amurka sun kawo ƙarshen kashe-kashen Kiristoci a Najeriya ta hanyar matakan soji da gwamnatin sa ta ɗauka kan ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya.

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi iƙirarin cewa sojojin Amurka sun kawo ƙarshen kashe-kashen Kiristoci a Najeriya ta hanyar matakan soji da gwamnatin sa ta ɗauka kan ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya.

Trump ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin wani taro a birnin Washington, inda ya yi magana kan nasarorin gwamnatinsa wajen yaƙi da ta’addanci a sassa daban-daban na duniya.

A cewarsa, matakin da Amurka ta ɗauka a Najeriya ya taka muhimmiyar rawa wajen dakatar da hare-haren da ake zargin ana kai wa al’ummomin Kiristoci, musamman a yankunan da ke fama da matsalar ta’addanci.

Ya ce kafin wannan mataki, dubban mutane da suka haɗa da mata, yara da tsofaffi sun rasa rayukansu a munanan hare-hare.

Trump ya kuma yi iƙirarin cewa farmakin da sojojin Amurka suka kai ya raunana ƙungiyoyin da ke da hannu a hare-haren, inda ya ce an kashe shugabansu da mataimakansa, lamarin da ya sa sauran mayaƙan suka ja da baya saboda tsoron ƙarin hare-hare.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments