Dakarun rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) sun ceto ɗalibai da malamai 10 da ake zargin mayaƙan ISWAP sun yi garkuwa da su yayin da suke rubuta jarabawar NECO a garin Lassa, ƙaramar hukumar Askira/Uba ta jihar Borno.
Rahotanni sun ce maharan sun kai farmaki makarantar sakandaren kimiyya da fasaha ta Lassa da safiyar Litinin, inda suka sace ɗalibai da malamai kafin su tsere zuwa cikin daji.
Bayan samun rahoton harin, rundunar Operation Hadin Kai ta ƙaddamar da samamen ceto tare da amfani da sa ido daga sararin sama, lamarin da ya kai ga fafatawa da ‘yan ta’addan a yankin Daggu.
Sojojin sun yi nasarar kashe da raunata wasu daga cikin maharan, tare da tilasta musu watsi da wasu daga cikin mutanen da suka sace.
Mutane 10 da suka haɗa da ɗalibai da malamai an ceto su ba tare da sun samu munanan raunuka ba, kuma suna samun kulawar likitoci