Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kashe manoma shida yayin da suke gudanar da aikinsu a gonaki a yankin Kujijiro, gundumar Kuyello, cikin ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.
An ce lamarin ya faru ne lokacin da manoman ke noma, inda maharan suka kai musu farmaki tare da hallaka su.
Ƙungiyar Cigaban Masarautar Birnin Gwari ta tabbatar da aukuwar harin, tana mai bayyana lamarin a matsayin abin takaici da ya sake nuna matsalar rashin tsaro da ke addabar yankin.
Rahotanni sun ce al’ummar yankin na ci gaba da kira ga hukumomin tsaro da su ɗauki matakan gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.