Saturday, October 17, 2026
HomeTsaroYan bindiga sun hallaka manoma shida a gonaki a Kaduna

Yan bindiga sun hallaka manoma shida a gonaki a Kaduna

Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kashe manoma shida yayin da suke gudanar da aikinsu a gonaki a yankin Kujijiro, gundumar Kuyello, cikin ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

An ce lamarin ya faru ne lokacin da manoman ke noma, inda maharan suka kai musu farmaki tare da hallaka su.

Ƙungiyar Cigaban Masarautar Birnin Gwari ta tabbatar da aukuwar harin, tana mai bayyana lamarin a matsayin abin takaici da ya sake nuna matsalar rashin tsaro da ke addabar yankin.

Rahotanni sun ce al’ummar yankin na ci gaba da kira ga hukumomin tsaro da su ɗauki matakan gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments