Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta tsare fitacciyar ’yar TikTok, Fati Cele, bayan mutuwar wani matashi da ake zargin saurayinta ne a gidanta.
Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwar murya da ya aikewa jaridar Punch a ranar Asabar.
Sai dai ya ce ba zai yi karin bayani kan lamarin ba a halin yanzu, domin ana ci gaba da gudanar da bincike.
Fati Cele, wadda ke zaune a unguwar Dan Bare a Kano kuma ’yar asalin Jihar Borno ce, na daga cikin fitattun masu amfani da TikTok.
Wani shaidu da ya nemi a sakaya sunansa ya ce mamacin ya fito daga gidan yana neman agaji bayan da wata gobara ta tashi a cikin gidan.